- Friday sermon by Imam Murtada Gusau in Hausa for Hausa readers
Daga Hudubar Imam Murtada Muhammad Gusau,
Masallacin Juma’a da ke anguwar Nagazi, Okene, Jahar Kogi.
HUDUBA TA FARKO:
Lallai dukkan godiya da kyakkyawan yabo sun tabbata ga Allah Wanda ya shiryar da mu zuwa ga tafarki madaidaici ba mu kasance masu shiryuwa ba da ba domin ya shiryar da mu ba.
Kuma ina shaidawa lallai ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bashi da abokin tarayya. Yana hukunta abin da yaso, kuma yana aikata abin da yayi nufi.
Kuma ina shaidawa lallai shugaban mu Annabi Muhammdu (saw), bawan sa ne kuma manzonsa ne; ya isar da manzanci, kuma ya rike amanar da Allah ya dora masa da gaskiya, kuma yayi nasiha ga al’ummah. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan sa da sahabban sa, da duk wadan da suka bisu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Lallai ina yi muku wasiya da ni kai na da jin tsoron Allah (swt), domin babu tsira a nan duniya da kuma lahira, sai da tsoron Allah, kuma tsoron Allah shine tushen dukkan Alheran duniya da lahira.
Ya ku’yan Najeriya! Lallai idan ba ku manta ba, idan zaku iya tunawa, a kan wannan mimbari mai albarka an sha tunatar da ku tare da jawo hankalin ku a kan al’amarin shugabanci, hadarin sa da kuma muhimmancin zaben mutanen kirki, masu amana, masu kishin talakawan su, Nagartattu a kan shugabancin. To, har wayau ma ba mu gaji ba, kuma in Allah yaso ba zamu gajiya ba, ba zamu yi kasa a gwiwa ba da yardar Allah, zamu ci gaba da bayani, zamu shiga lungu-lungu, sako-sako, rariya-rariya, gari-gari, kauye-kauye, majalisa-majalisa, gida-gida, titi-titi, kasuwa-kasuwa da dukkan wata mahada da matattarar Jama’a domin mu wayar wa al’ummah da kai a kan abin da ya kamata suyi game da nauyin da Allah ya dora musu na zaben shugabanni na gari masu kishin kasa da Al’ummah.
Ya ku ‘yan Najeriya! Ya kamata mu sani, idan kuwa mun sani mun manta ne, to ya kamata mu tuna, cewa a halin yanzu muna da kasa da wata shida a nan gaba domin tunkarar zaben dubu biyu da sha biyar (2015). Idan har ba muji tsoron Allah mu kayi abin da ya kamata ba na zaben nagartattun shugabanni a 2015, wallahi ina mai tabbatar muku (Allah ya kiyaye) cewa abin da muke ji, muke gani a yau na bala’i talauci, zubar da jini, cin hanci da rashawa, sokonci, rashin iya shugabanci, raba kan ‘yan kasa da sunan addini ko kabi lanci, rashin hadin kai da sauran su, zai zama wasan yara. Kuma ba zubar da hawaye ba wallahi idan ba muyi hankali ba (Allah ya kiyaye) har kukan jini sai mun yi.
Gashi nan dai, ya bayyana a fili, duk abin da muke gaya wa mutane ya fito fili karara. Kowa dai yana kallo kuma yana jin abin da ke gudana a wannan kasa tamu mai albarka Najeriya. Saboda haka, yanzu ya rage namu, ko dai mu sadaukar da duk abinda Allah ya hore muna na ilimi, dukiya, karfi, lokaci, wayo, dabara, hankali, gogewa da sauran su, mu kwaci kasar nan daga rugujewa, mu ceto ta daga rubabben shugabancin danniya, rashin kwarewa da fir’aunanci da duk duniya ta shaida da hakan kuma ta tabbatar, ko kuma wallahi dukkan mu sai munyi da na sani.
Idan har muka ci gaba da zama sokwaye, makwadaita, marasa kishin kasa da al’ummah, to ya rage namu. Kuma wallahi jiki dai magayi. Wanda kuwa bai ji bari ba to yaji hoho.
Saboda haka, ‘yan siyasa, sarakuna, malamai, fastoci, shugabannin addini na musulmi da kirista, ‘yan kasuwa, shugabannin al’ummah, talakawa musulmi da kirista, jami’an tsaro, maza da mata ‘yan Najeriya da sauransu, ku sani, wallahi hakkin ceton kasar nan ya rataya a wuyan ku. Ku manta da kwadayin abin duniya, ku manta da bambance-bambance, mu hadu muyi aiki tare, domin ganin wannan kasa tamu mai albarka ta dawo yanda take a da. Mai mutunci, zaman lafiya da kwarjini a idon duniya.
Ku sani ya ku ‘yan uwa masu girma! Bala’i, talauci, masifa, babu ruwan su da ko kai waye. Babu ruwan su da ko kai musulmi ne ko kirista, sannan babu ruwan su da yaren ka, jihar ka ko yankin da ka fito.
Ya ku ‘yan Najeriya! Don Allah ku kalli yanda kasar mu ta zama a idon duniya a yau, ku kalli yanda mutuncin jami’an tsaron mu ke neman zubewa. An ki a basu kyakkyawar kulawar da ta dace da kayan aiki domin tunkarar matsalar rashin tsaron da ke addabar kasar mu. Ku kalli yanda rayuwar dan Adam ta zama arha a kasar nan sakamakon rashin shugabanci nagari da zai kare rayuka da dukiyoyin Al’ummah.
Shin zamuci gaba ne da dora maslahar mu a saman maslahar al’ummah baki daya? Wai shin don Allah me ke damun mu ne? Wadanne irin mutane ne mu ‘yan Najeriya? Ta yaya zamu yi ta cika masallatai da coci-coci kullum da sunan ibada, amma duk yana neman ya zama na banza, saboda mun kasa hada kai mu tabbatar da shugabanci na gari a kasarmu, har aka wayi gari kasar mu na neman zama abin dariya a idon duniya? Don Allah meye duniya da dukkan abinda ke cikin ta ne? Shin mun manta cewa dukkanin mu zamu mutu mu bar duk abinda muka tara a nan duniya? Mun manta zamu tashi a gaban Allah gobe kiyama mu amsa tambayoyi a kan yanda muka aiwatar da rayuwar mu a wannan duniya?
Ya ku ‘yan Najeriya! Ku sani, lallai wallahi shekarar 2015 ita ce shekarar da zamu gane cewa shin munyi hankali ko kuwa har yanzu muna nan gidadawa sako tumaki balle jakai? Itace shekarar da zamu gane, shin mun koyi darussa a jikin da muke ji a wannan kasa, ko kuwa har yanzu bamu gane komai ba? Ita ce shekarar kwatar kai, shekarar gwajin dafi. Ita ce shekarar da indai har bamu samar da canji a wannan kasa ba, to babu lokacin da zamu iya samar da shi. Don haka kuwa ya rage namu, ga fili ga mai doki.
Ya ku‘Yan Najeriya sama da miliyan dari da saba’in! Ya ku musulmi! Lallai mu sani, gyaruwar al’ummah ta ta’allaka ne a kan gyaruwar shugabanni, kuma lalacewar al’ummah ya ta’allaka ne a kan lalacewar shugabanni. Abin nufi a nan shine; a duk lokacin da shugabanni su ka zama na kirki, masu kishin kasa da al’ummar su, to ana sa ran mutane ma za su zama na kirki, haka duk lokacin da shugabanni suka zama na banza, tanbadaddu, to lallai mutane ma haka zasu kasance domin a inda akuyar gaba tasha ruwa, ta baya ma idan ta zo nan zata sha. Shi yasa addinin musulunci ya ba da muhimmanci sosai a kan cewa lallai jama’a suyi kokarin ganin wadanda zasu zaba su jagorance su mutanen kirki ne ba ashararai ba, adilai ne ba azzalumai ba, yin haka zai sa zaman lafiya, da ci gaba su yawaita a kasa, soyayya da kaunar juna ya watsu a koina a kasa.
Ya ku Musulmi! Hakika Annabi (saw) ya bada labari cewa; “Yana daga alamomin tashin al-kiyama; ya kasance ana shugabantar da mutanen banza, jahilai, wadanda ba sa neman shiriya da littafin Allah da kuma Sunnar manzon sa (saw), sannan kuma ba sa jin nasiha, kuma ba sa wa’aztuwa, ba sa kwatanta adalci a tsakanin ‘yan kasa kuma ba sa daukar shawara.”
Al-Imamu Ahmad da Al-Bazzar sun ruwaito hadisi daga Jabir dan Abdullahi Allah ya kara yardar sa a gare shi, yace; “Lallai Annabi (saw) wata rana yace wa ka’ab bin ujrata Allah ya kara yarda a gareshi; “Allah ya tsareka ya kiyaye ka ya kai ka’ab daga riskar shugabancin mutanen banza, jahilai wawaye; sai ka’ab yace; menene shubagancin mutanen banza wawaye ya manzon Allah? Sai Annabi yace; “wasu shugabanni ne da zasu zo nan gaba bayan na wuce, ba sa bin shiriya ta, kuma ba sa bin tafarki na.
Saboda haka duk Wanda ya gaskata su a Kan karyar su kuma ya taimake su a Kan zaluncin su, to ba ya tare dani, kuma nima bana tare da shi, kuma ba zai taba shan ruwan tafki na ba. Kuma duk Wanda bai gaskata su a Kan karyar su ba kuma bai taimake su a Kan zaluncin su ba, to wadannan suna tare da Ni, kuma nima Ina tare da su, sannan kuma za su sha ruwan tafki na. Annabi (saw) yaci gaba da cewa; ya kai ka’ab bin ujrata! Ka sani Azumi garkuwa ne, kuma sadaka tana kau da zunubi, sallah neman kusanci ne zuwa ga Allah, ko kuma hujja ce; ya ka’ab bin ujrata; ka sani duk wata tsoka da ta ginu da haramun, to har abada ba za ta shiga Al’jannah ba, kuma wuta ita tafi cancantar ta, ya ka’ab bin ujrata; a kullum mutane suna yin sammako, akwai wanda zai sayar da Rayuwarsa, haka akwai wanda zai ‘yan to ta, ko ya halakar da ita.” (Ahmad da Bazzar ne suka ruwaito)
Ya ku mutane! Ku sani, shi mutumin banza, jahili, shine mai karancin hankali, mai karancin tunani, mara hangen nesa, wanda ko kansa ba zai iya shugabanta ba, ba zai iya shugabantar iyalin sa ba, balle ya shugabanci wanin sa. To ya ‘yan uwa, irin wannan mutum ya za’ayi ya shugabanci sama da mutane miliyan dari da saba’in? Zai yi kam, idan har ‘yan kasa sun yi sakaci, amma kasar kam za ta susuce, ta tabarbare ta lalace.
A wani hadisin na daban, Annabi (saw) yace: “Alkiyama ba za ta tsayu ba har sai ya kasance munafukan cikin al’ummah da wawayen ta su ne za su yi shugabanci”. (Dabarani ne ya ruwaito shi)
Munafukai da wawaye za ka same su masu karancin imani, masu karancin tsoron Allah, makaryata, Jahilai, Azzalumai, mayaudara, barayi, mara sa imani da tausayi, wadanda kan su kawai suka sani, sai ‘ya ‘yan su, iyalan su da abokan su. Babu ruwan su da sha’anin talakawa da al’ummah. Indai har jifa ta wuce kansu, to ta fada kan uban kowa.
Ya ku bayin Allah masu girma! Lallai idan aka wayi gari masu mulkin mutane, shugabannin su, jagororin su, sun kasance ashararai, mutanen banza, jahilai, wawaye to lallai al’amarin su zai lalace! Sai a wayi gari ana girmama mutanen banza a gwamnatin, ana kuma wulakanta mutanen kirki. A yarda da mayaudara, a wulakanta masu amana, sai ya kasance jahilai, marasa mutunci, tsageru, ‘yan ta’adda wadanda suka kware wajen iya cuta, magudi sharri sune masu fada aji a gwamnatin, masana kuwa dattawa mutanen kirki basu da bakin Magana, domin ko sun yi Magana ba ta da tasiri da matsayi a gurin gwamnatin, saboda gwamnati ce ta ‘yan iska gwamnati ce ta barayi, ‘yan ta’adda, mashaya jinin dan Adam, ‘yan giya, marasa mutunci.
Babban malami Al-Imamush-Sha’abiy Allah ya jikansa da rahama yana cewa; “Al kiyama ba za ta tsayu ba har sai an wayi gari ilimi ya koma ana kallon sa Jahilci, Jahilci kuwa ana kallon sa shine ilimin”. Wannan kuwa duk zai faru ne a cikin wannan zamani, da Al’amurra suka birkice, suka lalace, suka rincabe aka rasa shugabanni na gari, dattawa.
Kuma Annabi (saw) ya fada a hadisin Abdullahi dan Umar Allah ya kara yardar sa a gareshi, cewa; “Lallai yana daga Alamomin kusantowar Al kiyama; za’a dankwafar da mutanen kirki, kuma a daukaka mutanen banza ashararai”. (Al-haakim ya ruwaito shi a al-mustadrak)
Ya ku ‘yan Najeriya! A yau duk Wanda yake raye ya tabbatar kuma shi shaida ne a kan cewa lallai duk abinda Annabi (saw) ya ba da labari shine yake faruwa. Domin an wayi gari mafi yawancin wadanda ke shugabantar mu ashararai ne, sai fa ‘yan kadan daga cikinsu (Domin ba’a taruwa a zama daya). Duk yadda al’amari ya kasance ba’a taruwa a zama daya, kuma ba’a rasa na kirki a koda yaushe cikin shugabanni. Sannan ya zama wajibi a garemu lallai kowa yayi kokari yaga cewa ya ba da gudummawa gwargwadon ikon sa, domin ya zama wadanda za su shugabance mu a nan gaba, (musamman a zaben 2015) mutanen kirki ne. ‘Yan uwana ‘yan Najeriya! Mu sani, wallahi lokacin yin shiru ya wuce, ba zai yiwu ba ace mutanen banza ke jagorantar mu.
Ya ku ‘yan Najeriya! Mu sani, Lallai dukkan mu Allah (swt) zai kama mu da laifin rashin tabuka komai, a kan samarwa Al’ummah Nagartattun shugabanni. A yau dai dukkanin mu masu shaida ne a kan irin halin da kasarmu mai albarka, da yankin mu mai albarka na arewa suka shiga, sakamakon rashin shugabanci na gari. To dai abinda ya faru ya riga ya faru, yanzu abin tambaya a nan shine; me mukeyi domin kokarin samar da shugabanni na kwarai, na gari, masu amana? Ko har yanzu barcin muke yi ba mu farka ba?
Ya ku bayin Allah! Mu sani, lallai asalin shugabanci ko jagoranci, shine; a shugabantar da wanda ake ganin ya dara kowa ilimi, adalci, gaskiya, amana, lafiya, rashin nuna bambanci a gurin ‘yan kasa, mai kokarin hada kan ‘yan kasa, rashin son kai, mai kishin kasa, gogagge, gwarzon namiji, jarumi da sauran su. To amma a yau abin ba haka yake ba domin fasikai, mutanen banza, ashararai, mayaudara, mashaya, mazinata, barayi, wadanda basu san kimar dan Adam ba ke shugabantar mu. Don saboda suna da kudi, ko don dangartakar su, ko wani matsayi da suke dashi, ko saboda tsabagen rashin kunyarsu, ko don su ‘ya ‘yan manya ne, amma ba domin cancanta ko dacewa ba. Duk wannan saboda lalacewar al’amura ko kuma mutanen kirki sun yi saranda, sun rungume hannuwa, sun zama matsorata, sun mika wuya, sun ce su babu ruwan su da siyasa, sun yarda mutanen banza sun ci su da yaki.
Ya ku ‘yan Najeriya! Awf bin maalik ya ruwaito Hadisi cewa, Manzon Allah (saw) yace, “Mafifitan shugabannin ku sune wadanda ku ke kauna suke kaunar ku, ku ke yi musu addu’ar fatan alheri su ma su na yi muku. Sannan mafi lalacewar shubagannin ku, su ne wadanda ku ke fushi da su su ma suna fushi da ku, kuna la’antar su, su na la’antar ku”. (Muslim ne ya ruwaito)
Saboda haka ya ku Al’ummah! Wallahi lallai ya zama wajibi a garemu dukkan mu, manyan mu, shugabannin siyasar mu, sarakunan mu, shugabannin Addinan mu, manyan masu kudin mu da ‘yan kasuwar mu, ‘yan Bokon mu, talakawan mu, jami’an tsaron mu, ‘yan Jaridar mu kai da dukkan wani mai ruwa da tsaki a gurin samar da shugabanci na gari a kasar nan, mu hada hannu, mu hada karfi da karfe domin mu ga cewa lallai wannan kasa tamu mai Albarka (Najeriya) ta samu shugaban ci na gari. Idan ba haka ba kuwa, wallahi dukkan mu Allah (swt) zai kama mu da laifin yin sakaci, kuma ya Azabtar da mu gobe alkiyama.
Saboda haka ya ku ‘yan uwa muji tsoron Allah! Ya ku muminai mu koma ga Allah! Mu nemi kusancin mahaliccinmu yaku mutane! Mu roki Allah shiriya, da tabbatuwa a kan gaskiya, mu tuba zuwa ga Allah baki daya ya ku muminai! Ko ma samu rabauta.
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai, ka taimaki Najeriya da ‘yan Najeriya, ka taimake mu da shugabanni masu tsoron ka, ka kaskantar da kafirci da kafirai, ka halakar da makiyanka makiya Addinka, marasa kaunar zaman lafiya, ka taimaki bayinka salihai masu gaskiya, a duk inda suke, ka ruguza gungun munafunci da munafukai.
Ina fadar wannan Magana tawa, ina mai neman gafarar Allah a gare ni da ku, da dukkan sauran musulmi da duk wani mutumin kirki daga dukkan zunubi da kuskare, ku nemi gafarar sa, lallai shi mai gafara ne mai jinkai.
HUDUBA TA BIYU:
Bayan yabo da godiya ga Allah.
Ya ku Bayin Allah! Lallai na daga cikin abin da hudubar mu ta yau ta ke yin tsokaci a kai shine; “ba za ka taba samun mutanen kirki masu gaskiya suna zabe ko goyon bayan zulunci da shugabanni Azzalumai ba”.
Ya ku bayin Allah masu girma! Mu sani, Allah (swt) yayi umurni da adalci, da goyon bayan adilai a duk inda suke, sannan a daya gefen kuma yayi hani da zalunci da kuma juya wa zalunci da azzalumai baya a duk inda suke. Allah (swt) ya fada a littafinsa mai girma yana cewa:
“Lallai Allah yana yin umurni da adalci da kyautatawa da umurni a bai wa ma’abucin zumunta, kuma yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci. Yana yi muku gargadi, tsammaninku kuna tunawa”. (An-Nahli: 90)
Sannan Allah (swt) yana cewa:
“Kada ku karkata (ku goyi baya/ko ku zabi) zuwa ga wadanda suka yi zalunci sai wuta ta shafe ku (tare da su). Kuma ba ku da wadansu majibinta baicin Allah, sannan kuma ba za’a taimake ku ba”. (Hud: 113)
Ya ku musulmi! Lallai cikin wadannan ayoyi masu girma, mun ga yanda Allah (swt) ya umurce mu da tsaida adalci da kuma cewa kar mu yarda mu goyi bayan azzalumai. Mahaliccin mu ya tabbatar muna da cewa in har mu ka ki bin umurninsa to lallai Azabar wuta za ta shafe mu tare da azzaluman da muka goyi bayansu.
Ya ku bayin Allah! Mu kalli rayuwar mu a yau, shin muna bin umurnin Allah kuwa? Kalli yanda kiri-kiri zaka ga mutum ya goyi bayan azzalumi ba don komai ba, wai sai don Jam’iyyar su daya, ko yaren su daya, ko addinin su daya, ko garin su daya, ko Jahar su daya, ko kasar su daya, ko yanki daya su ka fito. Shin wannan mummunar dabi’a zaka same ta a gurin mutumin kirki kuwa? Yau an wayi gari ba mu kyamar zalunci da azzalumai saboda kwadayin abin duniya da son zuciya.
Yan uwa musulmi masu girma! Mu kalli yanda zaluncin cin hanci da rashawa suka yi katutu a wannan kasa tamu Najeriya, ta yanda Allah (swt) ya albarkaci wannan kasa, da dukkan nau’in albarkatu, amma saboda zalunci da cin hanci da rashawa da rashin adalcin shugabanni, an wayi gari kasar tana neman rushewa. A yau ko wane fanni ka duba za ka ga ba inda zalunci bai yi katutu ba. To bayan wannan, babban bala’in ma shine goyon bayan masu zaluncin don abin duniya, ko don wata maslaha (interest) ta mutum. Sai wannan ya jawo ba’a gudun aikata zalunci, domin mutane sun san duk zaluncin da za suyi, duk satar da za suyi, matukar suna da abin hannu, to al’umma za ta karbe su hannu bibiyu, a girmama su, a basu sarautar gargajiya ko digirin girmamawa ko wani matsayi a cikin al’ummah.
Saboda haka ya ku ‘yan uwa ku sani, lallai idan aka wayi gari al’ummah ta zama haka, to sai dai ace Allah ya kiyaye, domin tabbas Allah (swt) zai jarabi wannan al’ummah da abubuwa marasa dadi iri-iri masu tarin yawa, kamar yanda mu ke gani a yau. Allah ya kare mu Amin.
Ya ku ‘yan Najeriya! Lallai dole sai mun hada karfi da karfe, mun hada hannu, muyi aiki tare, kowa ya bada gudummawa gwargwardon karfin sa da ikonsa, domin mu kauda mulkin danniya, zalunci da azzulumai a tsakankanin mu, domin babban laifi ne mu sa ido, muyi shiru mu rungume hannuwa ana aikata zalunci, ba mu yi komai ba. To ba ma yin shirun ba, a’a, an wayi gari wasu daga cikin mu har goyon bayan zaluncin da azzalunmai su ke yi, saboda masu yin zaluncin ‘yan uwan su ne, ko addinin su daya, ko yaren su daya, ko jam’iyyar su daya, ko garin su daya, ko Jahar su daya, ko yanki daya suka fito, da sauran su. Lokaci yayi yaku bayin Allah! Da za mu daina kuma mu dakatar da wannan mummunar dabi’a a tsakanin mu domin Allah (swt) ya dube mu da idon rahama, kuma ya tausaya mana, ya kawo muna karshen wadannan bala’ oi da suka addabe mu musamman rashin tsaro da sauran su.
Ya ku musulmi! Mu duba fa saboda munin zalunci, Allah (swt) yace lallai ya haramta wa kansa zalunci, kuma ya sanya shi ya zama haramun tsakanin mu, saboda haka yace, kada mu zalunci juna. Amma duk mun manta da umurnin Allah, an wayi gari muna goyon bayan azzalumi saboda misali dan uwana ne, ko addinin mu daya, ko dan jami’yyata ne, ko yare na ne, ko kuma ba don komai ba sai don kwadayin abin hannun sa. Kuma da wannan mummunar dabi’a, wai mu ce mu musulmin kwarai, ne, ko muce mu mutanen kirki ne. shin muna nufin za mu yaudari Allah ne? Ya kamata mu shiga taitayin mu domin Allah ba abun wasa ba ne.
Ya ku bayin Allah! Al-Imam Ibn kathir (r) a yayin da yake bayani game da ayar nan da ta yi hani a kan goyon bayan azzalumai, da ke cikin suratul hud: 113, yace: “fadar Allah (swt),” kada ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku.” Ali bin talha ya ruwaito daga dan Abbas cewa, ma’anarsa: “kar ku mika wuya, kuyi saranda zuwa ga azzalumai”.
Kuma Al-Imam Al-Aufiy ya ruwaito daga Dan Abbas, cewa: ma’ anarsa shine, “karkata da goyon bayan shirka da zalunci”. Kuma Abul-Aaliyah yace, ma’a narsa, “kar ku yarda da aikin zalunci da ayyukan azzalumai.” Shi kuwa Al-Imam Ibn Jarir ya ruwaito daga dan Abbas, cewa, ma’anarsa: “kada ku karkata ku goyi bayan Azzalumai”. Daga karshe dai Ibn Kathir yace, zance mafi kyau game da fassarar wannan aya, shine; “kada ku taimaki azzalumai a kan zaluncin su, ta hanyar goyon bayan su. Domin duk wanda ya aikata haka, to ya yarda da aikin su na zalunci kenan”.
Ya ku musulmi masu sauraro! Lallai mu sani wannan aya ta kai matuka wajen hani a kan zalunci da kuma goyon bayan azzaluman shugabanni. To idan har Allah (swt) yayi tanandin azabar wuta ga wanda ya karkata ga azzalumai, ko yaya ne, to ina ga wanda yayi dumu-dumu cikin goyon bayansu ta hanyar yi musu kamfen na siyasa da sauransu don abin da zai samu a hannun su.
Ya ku musulmi masu girma! Lallai mu sani, ko shakka babu goyon bayan zalunci da azzalumai haramun ne, Allah ya hana. Sannan yana daga zunubai masu girma, (Al-Kabaa’ir). Domin Allah (swt) yayi alkawarin narkon azaba a kan wannan. Sannan mu sani, abinda kawai ya halatta muyi wa azzalumi, shine mu taimake shi, mu hana shi zaluncin, idan shugaba ne mu hana shi ci gaba da shugabancin ta hanyar da doka ta yi tanadi, wato lokacin zabe. Kamar yanda manzon Allah (saw) yayi umurni a hadisi ingantancce.
Sannan Al-Imam Al-Zamakhshari (r) yace: “Hani akan goyon bayan azzalumai ya hada da kar ka shiga cikin bin son zuciyar su, ka nisance su, kar ka yi abokantaka da su, kar ka zauna da su, kar ka ziyarce su, kar ka yi shiru a kan zaluncin su, kar ka nuna amincewar ka a kan zaluncinsu, kar kayi kamanceceniya da su, kar kayi kwaikwayon su ta kowace fuska, kar kayi kwadayin abin hannun su, kar ka yabe su har ka nuna cewa su masu girma ne, ko masu mutunci ne, sannan uwa uba kar ka nemar musu Jama’a da magoya baya (wato yi musu kamfen idan su ‘yan siyasa ne)”.
Kuma an hikaito cewa: “Babban malami daga cikin magabata da ake kira Al-muwaffiq, wata rana yana sallah a bayan wani limami, sai limamin ya karanta suratul hud, da ya kawo dai-dai aya ta 113 inda Allah (swt) ke maganar “kada ku karkata ku goyin bayan azzalumai, idan kunyi haka wuta zata shafe ku”, sai wannan bawan Allah (Al-muwaffiq) ya fadi kasa magashiyan ya suma, a lokacin da ya farfado sai aka tambaye shi, gafarta malam me ya faru ne? Sai yace, wannan ayar fa tana nufin Allah (swt) zai azabtar da wanda ya goyi bayan azzalumi ne, to ina ga azzalumin shi kansa? Sai yace wannan shi ne na tuna sai ya tsoratar dani, hankali na ya tashi yasa na suma”.
Saboda haka ya ku bayin Allah! Ya ku ‘yan Najeriya! Muji tsoron Allah, kuma mu sani wallahi ba zamu kawo karshen zalunci, ba har sai mun daina goyon bayan mulkin azzalumai mulkin danniya. Sai mun kyamace su da su da abinda suka mallaka. Amma muddin azzalumi zai yi zalunci ya tara abin duniya ta hanyar zaluncin, kuma daga karshe mu je muna kwadayin wannan abin nasa, muna girmama shi saboda abin duniya, to ba yanda za’a yi zalunci ya kare a cinkin al’ummah.
Ya ku ‘yan Najeriya! Ku sani, lallai zaben 2015 yana kusantowa, wannan lokaci mai matukar muhimmanci ga rayuwar mu, lokaci mai tsada yana karatowa. To abin tambaya a nan shine; wane irin shiri da tanadi muke yi domin zuwan wannan lokaci? Shin mun san muhimmanci da tasirin zaben shugabannin kwarai ga rayuwar mu kuwa? Shin zamu sake yarda da duk wani mayaudari kuwa? Shin zamu ci gaba da jefa rayuwar mu da ta ‘ya ‘yan mu da jikokin mu cikin hadari kuwa? Shin wai har yanzu barci muke yi ko kuwa mun farka? Shin zamu yarda muci gaba da rayuwa cikin kaskanci da wulakanci kuwa? Shin zamu yarda muci gaba da rayuwa irin ta bayi kuwa? Duk amsar wadannan tambayoyin da ire-iren su zamu fahimce su ne a zaben 2015, in har Allah yasa muna raye.
Mu duba yadda tsananin yunwa, fatara, talauci, cututtuka, rashin tsaro, da rashin ababen more rayuwa. Rashin hanyoyi masu kyau, rashin kyakkyawan ruwan sha, rashin magani a asibiti, rashin ingantattun makarantu, Jahilci, suke addabar mu a yau. Yara ba karatu, marasa lafiya ba kudin magani, addini ba kulawa, marayu da gajiyayyu an yasar da su, duk da irin dimbin arziki da masu arzikin da Allah ya hore wa kasar nan. Wai kuma a haka, a cikin irin wannan hali da yanayi ake son muyi fatar tabbatuwar wannan irin bakin mulki, mulkin da babu kwarewa, tausayi da imani a cikin sa.
Ya ku Jama’a! Lallai ya zama wajibi a kan dukkan wani dan Najeriya wallahi ya san cewa yayi wani abu domin samun canjin shugabanci a wannan kasa. Ya zama dole mu zabi shugaba adili, mai kishin kasa, mai son ‘yan kasa, mai kokarin hada kan ‘yan kasa, jarumi, gwarzo, mara tsoro, wanda ya fahimci kasar nan, gogaggen dan siyasa, wanda zai baiwa kowa hakkin sa ba tare da nuna bambancin addini ko na kabila ba. Dole ne mu zabi shugaba mai hankali, mai cika alkawari, mai daukar shawara, mai sauraron bukatu, koke-koke da matsalolin ‘yan kasar sa. Shugaba wanda zai kare rayuka, da dukiyoyin ‘yan kasar sa. Shugaba wanda zai ba kowa hakki da ‘yancin yin addinin sa ba tare da tsangwama ko nuna bambanci ba. Shugaba wanda zai yi kokarin wadata ‘yan kasa da kayayyakin more rayuwa. Shugaban da zai yi iya kokarin sa yaga cewa ya hana satar dukiyar al’ummah, ya hana cin hanci da rashawa. Shugaba wanda yake mai gaskiya, ba makaryaci ba. Shugaba mai bin doka, ba mai kama karya ba. Shugaba wanda ya fahimci cewa kasa da arzikin kasar na kowa da kowa ne ba na wani yanki kawai ba.
Ya ku ‘yan Najeriya! Lallai wallahi ku sani, irin wannan shugaban ba zai taba samuwa haka nan kawai ba tare da mun tabuka komai ba. Sai dukkanin mu mun aje son zuciyar mu, munyi aiki da hankalin mu da tunanin mu da wayon mu da basirar da Allah yayi muna. Sai mun manta da duk wani soki burutsu, shirme da sauran su, mu kalli cancanta da dacewa, musamman lura da halin da muke ciki, mu zabi shugaba managarci, gwarzo, gogagge, jarumi. Idan kuwa har munki ji, mun bi soye-soyen zukatan mu, to mu sani, wallahi, duk wanda yaki ji, to baya ki gani ba. Kuma lokaci ne kadai zai tabbatar muna da hakan.
Shi dai Allah ba ruwan sa, ya riga ya bamu dama, ya kuma bamu zabi, idan har muka yi amfani da damar nan ta hanyar da ta dace, mune zamu amfana, idan kuwa har mun banzatar da wannan dama, to dai mune zamu ci gaba da shan wahala. Allah ba zai sauko ya zabar muna shugabanni na kwarai ba, a’a wallahi mune za muyi, domin ya bamu zabi, don haka ya rage namu.
Ya kai dan uwa mai Albarka! Ka sani, lokacin zaunawa ka rungume hannuwa kace kai babu ruwan ka da sha’anin siyasa da shugabanci a Najeriya wallahi ya wuce, domin idan bala’o’i suna faruwa a kasa sanadiyyar rashin shugabanci na gari, baka isa kace babu ruwanka ba, domin sai ya shafe ka ko ya shafi wani naka tabbas. Sannan ka mutu ka hadu da Allah ya tambaye ka, shin me yasa baka bada gudummawa koda da zabe ne ko jefa kuri’a ko bayar da shawara domin tabbatar da shugabanci na gari a bayan kasa ba? Kaga sai ka shirya irin amsar da zaka bai wa Allah, mahaliccin ka. Nayi imani, ko kai musulmi ne ko kirista, ko marar addini, ko kai dan kudu ne ko dan arewa, lallai kana ji a jikin ka sanadiyyar wannan bakin mulki.
Ya kai dan uwa/‘yar uwa mai girma! Wallahi ba ka da/ ki da wata hujja da zaka/zaki kare kanka/ kanki da ita a gaban Allah gobe kiyama, a kan kasan da cewa mutum ba ya da kwarewa, wayewa da sanin ya kamatan da zai shugabanci kasa ko ya shugabanci al-ummah, amma kace kai dole sai ka goyi bayansa yaci zabe, ko kuma kace zaka zabe shi ko ka bashi kuri’ar ka don kawai kare maslaharka. Lallai ka sani, wallahi yin haka zai jawo maka matsala tun a nan duniya kafin kaje lahira. Saboda haka ya zama dole lallai muyi karatun ta natsu, mu canza tunani kuma muji tsoron Allah. Idan ba haka ba kuwa, to wallahi… sai ka karasa da kanka.
Muji tsoron Allah ya ku ‘yan Najeriya! Muji tsoron Allah yaku muninai! Mu nemi kusancin mahaliccin mu ya ku bayin Allah! Da tabattuwa a kan gaskiya da yakar zalunci da azzalumai, mu tuba zuwa ga Allah baki daya, ko ma samu rabauta.
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai, ka taimaki Najeriya da ‘yan Najeriya, ka kaskantar da kafirci da kafirai, ka halakar da makiyanka makiya addinin ka, wadanda basa son a zauna lafiya a Najeriya da duniya baki daya. Ka taimaki bayin ka salihai a duk inda suke, ka bamu ilimi mai amfani. Kuma ka nuna mana gaskiya ka bamu ikon bin ta, ka nuna mana karya, ka bamu ikon guje ma ta.
Ya Allah ‘yan uwan mu mutanen Jahar Borno, Yobe da Adamawa da Allah ya Jarabe su da fitintinu da tashe-tashen hankula, Allah ka kawo musu saukin wadannan wahalhalu. Ya Allah ka Jikan su, ka tausaya musu ka sa duk wannan wahala ta zama kaffara a gare su. Ya Allah ka albarkace su da mu baki daya da samun kwanciyar hankali da zaman lafiya. Ka wadata kasar mu ka zaunar da mu lafiya amin.
Ina fadar wannan Magana tawa ina neman gafarar Allah a gare ni da ku, da dukkan sauran musulmi daga dukkan zunubi da kuskure, ku nemi gafarar sa lallai shi mai gafara ne mai jin kai.
Ku tashi zuwa ga sallah ya ku bayin Allah! Ina rokon Allah ya tausaya muku, da ni baki daya.
Wassalamu alaikum,
Wannan hudubar jumu’a an gabatar da ita ne a yau juma’a 18, ga Zul-qi’idah 1435 A.H. (Satumba 12, 2014) daga dan uwanku Imam Murtada Muhammad Gusau, Babban limamin masallacin Juma’a na anguwar Nagazi Okene, Jahar Kogi, Najeriya. Za’a iya tuntubar sa ta: 08038289761 da murtadagusau2@gmail.com ko murtadagusau2@yahoo.com